12/06/2026
MACE MUTUM CE!(4)
Ci gaba kuma na karshe...
."Ba zai yiwu ba ka samu mutum da idanunsa biyu yana gani,ka ce masa...Kai..yanzu kai makaho ne,kuma kace dole sai ya yarda,kuma duk abinda zai fada ba abin kamawa bane,kawai dole ya hakura shi tunda ance baya gani to ya yarda kawai baya gani,...wannan ganin kuma ya sawa ransa cewa,sunansa makanta,..anya haka zai yiwu?
Kamar haka Al'umma su ka dauki mace,da iyawarta da kwarewarta da tunaninta da duk wata baiwa da Allah ya yi mata banza ne kawai, hujja ita mace ce.Wannan ba karamin zalunci bane.
BAMBANCIN KWAKWALWAR MACE DA TA NAMIJI TUN A YARINTA.
Idan ka tambayi mutane game da yayansu da su ke haifowa,ka tambaye su idan aka samu mace mai lafiyayyen tunani da namiji mai lafiyayyen tunani,za ka ga idan suna yara macen ta fi basira da gane abubuwa...amma tambaya..me ya sa namijin yake zama shine mai basira fiye da macen idan tafiya ta yi tafiya?
Dalili shine....su kansu iyaye suna sawwala idan su ka haifo mace ba komai bace namijin nan dai shine wata tsiya,haka za a rika gwasale mace duk abinda zata yi ana gaya mata ita macece,ba za ta iya ba sai maza,
Shi kuma namijin ana karfafarsa ana ce masa shi namiji ne zai iya yin kaza da kaza,wato tun a farko uwa da uba su ke kashe zuciyar yarsu mace..a duniyar hausawa kuwa tun tana zanin goyo ake fara gaya mata,amfaninta kawai a wannan duniyar shine..ta yi girki a ci,ta haifi yaya shikenan bata da wani cigaba da zata samarwa a al'umma,kuma ba'a da wani fata akanta wanda ya wuce ta girma ta yi aure.
Al'umar da ta ci gaba tana sanya mace a matsayi na gaba wajen gina Al'umma,shi yasa duk wasu abubuwa masu alaka da kwakwalwa ana barwa mata ne su, su ka san yadda ake gina dan'adam,...Misali...makarantu da yawa mata ne ke koyarwa,idan ma akwai maza zaka samu kadan ne a duniyar da aka ci gaba.
Anan suna nufin gina al'umma sai mata,tunda aka dauki abinda ya shafi ilimi aka mikawa mata shi,sannan da yawan mutanen da s**a zama wasu a kwakwalwa za ka samu iyayensu mata ne s**a basu gudunmawa 100%.
KISSAR IMAM ALI AS DA MU'AWIYA.
Ya zo a sira ta Imam Ali as cewa...
Mu'awiya ya taba aikawa Imam Ali as cewa,..dole Imam Ali aa ya zo ya yi masa bai'a,idan kuma ya ki zuwa,shi Mu'awiya zai turo masa mazaje masu zuciyar zakuna.
Sai Imam Ali as ya ce..ba zai masa bai'aba..kuma yana jiran zuwan wadannan mazajen masu zuciyar zakuna..zai hadasu da mazaje masu zuciyar mata.
Wannan Maganar ta shugaban balaga da hikma ta sa duniya ta shiga tunani,shin zuciyar mace yaya ta ke?
INA MATSALAR TA KE?
Dole mu yi nazari muga a ina muka samu wannan matsalar mai dogon tarihi,domin warwareta da abubuwan da su ke na zahiri.
Tabbas mata suna da rauni musamman rauni kala biyu,..
Akwai na halitta wanda Allah ne ya halicce su a haka,idan mu ka ce sai mun sauya su daga wannan dabi'ar zuwa tamu abu ne da ba zai yiwu ba...Misali,..sauya halittarsu ta rashin kuzari zuwa kuzari..tausayi zuwa rashin tausayi,..salo na jiki da ya ke banbance mace da namiji...
Tabbas duka wannan ba muna cewa ba zai yiwu bane gaba daya,ana iya yi amma natijar da za a samu za'aga ta yi muni sosai.
Akwai Dabi'ar da dora msu ita aka yi,wadda ita ce mu ke so a yaka,a sauyata...Misali...
Dakusar da tunanun mace,da nuna mata ita kamar Robot ta ke bama a so ta rika tunani,illa iyaka duk abinda aka gaya mata kawai ta bi.
Nuna mata ita bata da wani amfani da ya wuce haihuwa da tsaron gida da duk wasu ayyuka da su ka shafi cikin gida.
A bangaren hausawa,an sanya musu wani tsoro da aka kirkiro shi,daga mace ta fara ganin alamomin girma a tare da ita,hankalinta zai koma zancen gidan miji,an kayyade wasu shekaru da ake ganin idan ta wuce su bata yi aure ba rayuwarta ta shiga hatsari,sabida haka ko karatu take a lokacin tunaninta ya rabu biyu ne,fargabar samun miji sannan shi karatun bata san me ake yi da shi ba,dukda wasu suna dauka ana karatun ne dan sana'a,wanda alokacin ne ya kamata a da mata tunanin cewa,ita wata al'umma ce da duniya ke jira ta karaso wannan wurin domin amfanar mutane,sabida haka sai ya zama tunaninta wane amfani za ta yiwa al'umar da ta ke ciki?.
Sai ya zama wannan shine tunaninta,shi kuma aure ya zama wani abu ne na kamala wanda zai karfafeta zuwa cimma wancan burin,wato ta gane ba iya aure bane kawai amfaninta ga al'umma.
Sanya musu jin cewa,su bayi ne ko a gidan mijinsu,kuma shi gidan mijin tamkar kurkuku ya ke idan ka shiga kawai sai yadda miji ya fasalta maka rayuwa,duk ilimin da mace ta karanta yana aiki ne a waje,idan ta zo gida miji ne zai zabar mata cewa,..wannan shine ilimi wannan ba ilimi bane,wannan shine daidai wannan ba daidai ba..wannan fa ko da kasurgumin jahili ta aura shikenan zai zamar da ita irinsa,ba mu ce kada a yi wa miji biyayya ba,ko shi miji ya saki matarsa a t**i kamar kazar hausa,a'a,...Muna cewa a duba aga wace gudunmawa za su baiwa al'umma sai a karfafe su,idan aka yi hakan za a ga tasirinsa har a yayanda za a haifa.
Anan yana da kyau su maza su sani,sau da yawa suna rusa rayuwarsu ne da kansu ta hanyar daqile tunnin matansu wanda kuma wannan natijar na komawa kan yayansu.
TASIRIN IYAYE MATA A RAYUWAR YAYANSU.
Manazarta sun gano cewa,..Matan da aka fi basu dama da girmamawa tun daga tasowarsu a yarinta har zuwa gidanje aure,sun fi samar da yaya nagartattu masu hazaqa da tarbiyya kuma sun fi gane karatu ko a makaranta,sabanin matan da su ke rayuwa cikin kunci tun suna yarinta ,shi kuma kuncin nan babu kuncin da ya kai da iliminka da tunaninka a mayar da kai baka san komai ba,duk abinda ka ke ji a kwakwalwarka ba'a yarda da shi ba.
..."Za mu kawo cikakken bayani a rubutunmu mai taken..
HANYOYIN DA ZA KU GINA TUNANIN YAYANKU.
Haka nan macen da ta samu kulawa da nutsuwa da girmamawa tsufa baya kamata da wuri.
Sannan gwargwadon yadda ka baiwa mace dama a matsayinta na Mutum ,kai kanka mijinta za ka fi samun kulawar da ya kamata.
Sannan kuma ana samun soyayyar yaya ga iyayensu maza da su ke girmama iyayensu mata,saboda duk wannan yanayin da ka tafiyar da mace akai yana tasiri a kwakwalwar yaran da ta haifa tun daga ciki.
KARKAREWA.
Wannan rubutun yana kira ne ga al'umar da ta dauki mace tamkar ba mutum ba,ta yi mata matsaya cewa,bata da wani amfani daga aikace-aikacen gida sai haihuwar yara cewa,su sauya tunani yanzu duniya ta ci gaba ta gano cewa,MACE MUTUM CE,duk inda ka ke son ci gaba idan ka dora mace a wurin za a kai nasara matukar bai saba da asalinta na yadda Allah ya ajiyeta Mace ba.
Muna fatan Allah ya sa mu amfana da dan abinda muka ambata.
Nagode
Shareef Muhsan Bachirawa
08034318311
25/05/2026