18/08/2021
Slm
TARIHIN KUNGIYAR TALIBAN 👇👇 A TAKAICE 👇👇
📮 Daga; B Salia Sicey
Abinda A ke Nufi Da Taliban Shi Ne Dalibai, Ko Almajirai, da Yaren Pashto, wanda Yawanci Yan Kasar Ke Amfani Dashi,
Ƙungiyar Taliban wata kungiyar gwagwarmayar Islama ce da ke aiki a Afghanistan 🇦🇫 da yammacin Pakistan 🇵🇰 A ƙarshen shekarun 1990 ta kafa Gwamnatin Islama ta daular Musulunci ta Afghanistan🇦🇫 kuma kasar Pakistan 🇵🇰 Ta Taimaka mata. Amma Kasar Ta sha Musanta Hakan
Yan Taliban sun mulki Afghanistan tsakanin 1996 da 2001. A wannan lokacin, shugabanninta sun kafa tsauraran ƙa'idodin Shari'ar da ba a taɓa gani a duniyar Musulmi ba. Mafi yawan s**ar da aka yiwa ƙungiyar Taliban ya fito ne daga manyan malaman musulmai. Misali, idan aka k**a barawo ya Saci wani abu Taliban za ta Sa A yanke masa hannu daya don kar ya sake amfani da shi Don sake Yin sata, komai kankatar Darajar abin da ya sata. Yawancin masu laifi a na kashe su da Hanzari ba tare da an yi musu shari'a ba. Duk wanda ya ƙi bin doka an ɗauke shi a matsayin makiyin musulunci, 'Yan Taliban sun shahara a duk duniya saboda mummunar cutar da suke yi wa mata da' yan mata. Haka a mulkin Taliban Ajiye TV 📺Haramun ne, kuma dole kowanne matashi ya Ajiye Gemu, an haramta wakoki Fina-finai Da wasannin Ciki harda kwallon kafa, Mulkin Taliban A wancan Lokacin Bai sami amincewar Kasashen duniya ba, illa kasashe guda 3 da s**a aminta da su, kasashen su ne Pakistan 🇵🇰 UAE 🇦🇪 da kuma saudi Arabia 🇸🇦 A wani lokaci, 'yan Taliban sun yi barazanar hargitsa Pakistan daga yankunan da suke iko da su a arewa maso yamma. Wani Lokaci a Watan Oktoban Shekarar 2012, Ya Kungiyar Taliban Sun Harbi yar makaranta Malala Yousafzai a hanyarta ta komawa gida a garin Mingora. Na Kasar Pakistan 🇵🇰 Saboda sun tuhumeta da laifin shelar sa ya'ya mata a makarantun Boko
Bayan harin 11 ga Satumba a 2001, Amurka ta mamaye Afghanistan. 'Yan Taliban sun ba wa ƙungiyar Al-Qaeda mafaka inda za su yi aiyukan Ta'addanci Su Da Horar Da Sojojin Sa Kai, Gwamnatin Amurka ta ce Osama bin Laden da Kungiyar al-Qaeda ne s**a kai hare-haren a biranen New York da Washington, amma ‘yan Taliban din sun nemi Amurka da ta ba su Shaidar hakan kafin ta mika mata su. Manufar mamayar ita ce kawar da gwamnatin Taliban daga mulki, Da rusa al-Qaeda da kuma k**a Bin Laden. A ranar 7 ga Oktoba, 2001, kawancen sojan da Amurka ke jagoranta ya kaddamar da hare-hare a Afghanistan, kuma a makon farko na Disamba gwamnatin Taliban ta rushe. Shugaban kungiyar na wancan lokacin, Mullah Mohammad Omar, da wasu manyan mutane, ciki har da Bin Laden, sun gujewa kamu, Rahotanni sun ce da yawa daga cikin manyan shugabannin Taliban sun samu mafaka a birnin Quetta na Pakistan, Amma Pakistan 🇵🇰 ta musunta haka, Duk da yawan sojojin kasashen waje da yawa, sannu a hankali 'yan Taliban sun dawo sannan s**a fadada tasirin su a Afghanistan, inda s**a sanya dimbin yankunan kasar cikin rashin tsaro, tashin hankali a kasar ya koma matakin da ba a gani ba tun 2001.
Ana tunanin kungiyar yanzu ta fi karfi fiye da kowane lokaci tun lokacin da aka kore su a 2001, tare da mayaka 85,000 a cewar alkaluman baya -bayan nan na Nato.
NA TSAYA A NAN DON NA GAJI ✍ 😇