15/11/2017
ROGO CONCERN FORUM
Kungiya mai fafutukar
ganin ta kawowa
Karamar hukumar ROGO
cigaba ta kowanne
bangare.
A ranar Alhamis
09/11/2017, ta gudanar
da zama na musamman
da dukkanin 'yayanta
dake dukkan Mazabu
goma na wannan
Karamar Hukuma ta
ROGO. Angudanar da
taron ne a garin BELI.
Kungiyar ta shawarta
matsaloli da dama
wadanda s**a Addabi
wannan karamar
hukuma. Amman ta
Samu damar daukar
guda daya wanda
wannan Kungiya ta
kudiri aniyar ganin bayan
wannan Matsala.
Wutar Lantarki (NEPA).
Wacce itama matsalace
da ta dade da kafuwa a
wannan karamar
hukuma..
Cikin ikon Allah idan
NEPA ta dawo Karamar
hukumar Rogo zamu
kasance masu farin ciki,
ta hanyoyi da dama,
kamar:
* Amfanin Kamfanoni da dama
zasu samu saukin
aikace-aikace da saukin
sayen Mai domin
Zubawa injina.
* Sannan a bangare SADARWA, ka huta kashe kudin chaji na waya da kuma Radiyoyin zamani masu Amfani da Chaji, kallon labarai daga ko'ina a fadin Duniya, kallon Film cikin Sauki.
* Takan taimaka sosai wajen sanyaya kayayyakin da s**a danganci Ruwa. Tare da dumamawa ko kuma dafa Abinci duk a cikin sauki.
* dama Sauransu,
Kuma kungiya haryanzu a shirye take wajen ansar Shawarwari daga kowanne mutum, akan hanyar da za'abi domin kawo karshen matsalar wutar lantarki a fadin wannan Karamar hukumar ROGO.
Sing. S.S. RGG.